Gwamnatin tarayya ta ce kofa a bude take ga duk wani ci gaba da za a iya samu na samo maganin cutar korona da ta yiwa kasashen duniya katutu.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Laolu Akande.

Sanarwar ta ce mataimakin shugaban ya furta hakan ne a lokacin da yake magana a taron da wasu kamfanonin samarwa tare da sarrafa magunguna suka shirya ta fasahar zamani.

Ya ce tattaunawa da aka yi a tsakanin kamfanonin da gwamnatin tarayya na da matukar muhimmanci.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da ministan lafiya Osagie Ehanire da kuma shugaban hukumar samar da lafiya a matakin farko Faisal Shuaib.

A lokacin da yake magana daya daga cikin wakilan kamfanin ya ce Najeriya ce a sahun gaba cikin kasashen Afrika da kamfanin zai samar da magunguna.

A nasa jawabin ministan lafiya Ehanire, y ace gwamnatin tarayya za ta sanya ido kan yanda za a samar da magungunan da wadanda za su samar da kuma wadanda za su yi safarar magungunan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *