Kwamitin majalisar dattawa dake kula da harkokin kimiyya da fasaha ya bukaci gwamnatocin jihohi su hada hannu da cibiyar kula da kimiyya wajen samar da ayyuka a tsakanin matasa.

Kwamitin ya bukaci hakan ne a lokacin da shugabarsu Uche Ekwunife ya jagoranci tawagar zuwa wajen gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi.

Ekwunife ta ce akwai bukatar a samu hadin gwiwa a tsakanin gwamnatocin jihohi, kananan hukumomi da cibiyar wajen amfana da harkokin fasaha.

Kwamitin majalisar ta ce ta kai ziyara Enugu ne domin ganewa idanun ta dukkanin cibiyoyin hukumar da aka kafa a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Ta bukaci gwamnan da ya ci gaba da taimakawa cibiyoyin dake jihar ta Enugu domin samar da ayyukan yi tare da rage zaman kashe wando a tsakanin al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *