Kwamitin yaki da cutar korona karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari rahoton wucin gadi.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan jim kadan bayan kammala rahoton, ya ce shugaba Buhari ya nuna farin cikinsa da rahoton kwamitin.

A cewarsa dukkanin ‘yan kwamitin na yaki da cutar na da zummar gudanar da aikin da aka basu, kuma suna amfani da kwarewar da suke da ita wajen gudanar da aikin.

Sannan ya bukaci gwamnatocin jihohi su ci gaba da binciken wadanda ke dauke da cutar a tsakanin al’umma tare da tabbatar da cewa an basu kulawar da ake bukata.

Ya ce hakan na da matukar muhimmanci duba da cewa mutane sun kammala bukukuwan Babbar Sallah, kuma akwai fargabar kara yaduwar cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *