Shelkwatar tsaro ta Najeriya ta ce runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci da ake yiwa lakabi da Operation Delta Safe ta kai samame maboyar masu fashin teku da fasa bututun mai tare da kashe 6 daga cikin su.

Babban jami’in yada labarai da hulda da jama’a na rundunar sojin Majo Janar John Enenche ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Enenche ya ce rundunar ta yi amfani da bayanan sirri da ta samu daga wajen wasu kan maboyar shugaban masu fashin tekun, wanda ya tsere zuwa garin Fatakwal tare da rakiyar wani shahararren mai garkuwa da mutane.

Ya ce nan take jami’an sojin suka kai samame maboyar ‘yan ta’addan dake Tukugbene-Ayama a karamar hukumar Ijaw, inda suka kama mutanen tare da magoya bayansu.

A cewarsa kafin kama ‘yan ta’addan an samu musayar wuta da su inda suka nufo jami’an sojin a wasu jiragen ruwa da suka amfani dasu wajen ayyukan ta’addancin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *