Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta ba ‘ya’yanta umarnin ci-gaba da sayar da man fetur akan farashin naira 143 kowace lita har sai ta samu umarnin kara fashin man daga hukumar dake kayyade farashin man ta kasa PPPRA.

Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Suleiman Yakubu ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

A lokacin da yake maida martani kan tsohon farashin man na naira 138 kowace lita akan farashin baya na 132, Yakubu, ya ce kungiyar za ta bayyana sabon tsarin da zarar sun samu umarni a hukumance.

Wannan na zuwa ne bayan kamfanin matatar mai na kasa NNPC da Kamfani da ke kula da bututu da hada-hadar man fetur ta kasa PPMC sun bayyana naira 138 a matsayin sabon farashi.

Tuni dai Shugaban Kamfani na PPMC Mohammed Bello, ya ce sabon farshin man zai fara aiki ne daga ranar 5 ga watan nan na Augusta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *