Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bukaci masu kada kuri’a, jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da ‘yan takara da kuma masu ruwa da tsaki su bi ka’idojin kariya daga cutar korona a lokacin zabubbuka.

Shugaban hukumar Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan ne a lokacin da hukumar ke ganawa da manema da masu ruwa da tsaki gabannin zaben cike gurbi na jihar Nasarawa ta tsakiya.

Yakubu ya shawarci masu kada kuri’ar da su yi amfani da takunkumin rufe baki da hanci idan za su tafi rumfunan zabe, domin a cewarsa duk wanda bashi da takunkumin ba zai yi zabe ba.

Ya kara da cewa hukumar za ta yi amfani da na’urar tantance katin masu kada kuri’a, kuma za a samar da sinadarin tsaftace hanu da aka fi sani da sanitizer.

Yakubu ya kara da cewa hukumar ta gama gwaje-gwaje na na’urorin da za ta yi amfani dasu, yayin da aka kai kayayyaki masu muhimmanci cibiyar babban bankin dake Nasarawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *