Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce gwamnatinsa ba za ta bar matsalar tsaro da ta addabi jihar ta ta’azzara ba.

Masari ya furta hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar gwamnan karin jami’an soji dubu biyu da aka tura jihar sun nunawa ‘yan ta’addan irin shirin da gwamnatoci ke da shi wajen murkushe su.

Ya kara bada tabbacin cewa ayyukan ta’addanci ba za su taba hana gudanar da harkokin noma a jihar ba duba da cewa manoman da gwamnatin na da kudurin bunkasa harkokin noman.

Ya ce gwamnatin jihar za ta gyara wasu dam-dam guda 30 da suka lalace a jihar, tare da samar da wasu sabbi da kuma hanyoyin ruwa da makiyaya za su rika amfani dasu.

Masari ya ce sabbin matakan da aka dauka wajen magance matsalolin da suka addabi jihar.

Ya ce makasudin ganawar tasu da shugaban kasa Muhammadu Buhari, shine domin yi masa barka da Sallah, ganin cewa wannan shine karon farko a cikin shekaru 4 da suka gabata da shugaban bai je Sallah gida ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *