Daga Allah muka zo ga Allah zamu koma. A jiya Laraba 5 ga watan Agustar shekarqr 2020 ne Allah yayi wa shahararren dan jarida Ladan Ibrahim Ayawa rasuwa bayan yayi jinya a asibitin Goerge Washington da ke babban birnin Amurka.

Hazikin dan jaridar haifaffen garin Kontagora ne a jihar Neja inda ya girma. Sannan yayi digirinsa a Jami’ar Usmanu Dan Fodio da ke jihar Sokoto a Najeriya a fannin harshen Hausa.

Ladan dadadden ma’aikacin radiyo ne da ya shafe shekaru yana aiki a Radio Najeria har zuwa ritayarsa a wajen. Bayan nan ne kuma ya fara aiki da Murya Amurka a matsayin wakilinsu na Legas kafin daga bisani suka dauko shi aiki na dindindin a shelkwatar Muryar Amurka da ke birnin Washington DC.

Kafin ajiye aikinsa na Muryar Amurka, Ladan yana daga cikin masu gabatar da labarai da shirye-shiryen radiyo irin su Himma Bata Ga Raggo da sauransu. Duk wanda ya taba aiki ko hulda da Ladan zai fada cewa shi mutum ne mai hakuri da sanin ya kamata ga son addini. Ya rasu ya bar matarsa daya da ‘ya’ya matasa guda uku.

A madadin daukacin ma’aikatan Radiyon Talaka, muna mika sakon ta’aziyyarmu ga ‘yan uwa da abokan arzikin Marigari Ladan Ibrahim Ayawa da fatan Allah ya ji kansa ya kuma kyautata karshenmu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *