Fadar shugaban kasa ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa gwamnatin tarayya ta dauki wasu tubabbun ‘yan Boko Haram aikin soji.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce ba wani ko mutum gudu daga cikin tubabbun ‘yan Boko Haram 601 da aka koyawa sana’o’i tare da sauya musu tunani da aka dauka aikin soja.

Shehu ya kara da cewa ba wani shugaba na kwarai ko dan kasa na kwarai da zai amince a irin wadannan jita-jitan da ake yadawa musamman a shafukkan sada zumunta.

Ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnati ce dake da kaifin tunani, kuma ta san illar ayyukan ta’addanci dan haka ba za ta yi wani abu da zai kawo matsala ga kasa ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *