Gwamnatin tarayya ta ce daga yanzu duk wanda aka samu da laifin furta kalaman kiyayya zai biya tarar Naira miliyan biyar.

Ministan yada labaran Lai Mohammed ya bayyana a Abuja, yayin da ya ke kaddamar da kwaskwarimar da aka yi wa dokar watsa labarai ta Nijeriya.

Ya ce ya dauki matakin ne bayan samun amincewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya bukaci a sauya dokar sakamakon irin kalaman kiyayya da ‘yan Nijeriya su ka rika yi a lokaci da kuma bayan zaben shekara ta 2019.

A baya da wasu manyan jami’an gwamnati da uwar gidan shugaban kasa A’isha Buhari, sun koka da yadda wasu ‘yan Nijeriya yada kalaman kiyayya da jita-jita, su na masu yin kira da a sa ido a kan yadda ake amfani da shafukan sada zumunta.

Lai Mohammed, ya ce sabuwar dokar ta hukumar da ke kula da harkokin watsa labarai, ta yi garambawul a kan yadda ake watsa labarun siyasa da na cikin gida da labarun da ke faruwa kai-tsaye da tallace-tallace da kuma yaki da halayyar goyayya tsakanin kafafen watsa labarai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *