Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya jinjina wa manyan hafsoshin tsaron Nijeriya bisa kokarin da su ke yi wajen kawo karshen ayyukan ta’addanci a Nijeriya.

Bayan ganawa da ya yi da manyan hafsoshin tare da mai ba shi shawara ta fuskar tsaro, Buhari ya ce hafsoshi sun cancanci a yaba masu bisa ayyukan samar da tsaro da su ke yi a Nijeriya, sai dai ya ce dole a sa himma wajen ganin an gama da burbushin ‘yan ta’addan da su ka rage a Nijeriya.

Mai ba shugaba Buhari Shawara ta fuskar tsaro Babagana Monguno, ya ce Buhari ya gamsu da yadda manyan jami’an tsaron Nijeriya ke gudanar da ayyukan su na samar da tsaro.

Shugaba Buhari, ya ce abin da ya fi damun sa shi ne alkawuran da su ka yi wa ‘yan Nijeriya cewa za su samar da tsaro, don haka  ya bada umurnin a yi wa fannin tsaron Nijeriya garambawul, sannan ya umarci manyan hafsoshin Nijeriya su sauya salon yaki da su ke amfani da shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *