Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS, sun kama Olawale Bakare da wasu sauran mutane shida da ke sanye da huluna ruwan dorawa yayin da su ka fito gudanar da zanga-zangar juyin juya hali.  

An dai kama matasan ne a yankin Olaiya da ke Osogbo babban birnin jihar Osun, yayin da Matasan a karkashin jagorancin Bakare su ka yi tattaki zuwa ofishin ‘yan jarida domin gabatar da jawabi a kan zanga-zangar da su ka fara.  

Bayan matasan sun taru a gaban ofishin ‘yan jaridar domin a yi masu iso, sai wasu ‘yan sanda su ka same tare da fara tattaunawa da su, daga bisani wasu jami’an tsaro na hukumar DSS su ka yi awon gaba da su.

Haka kuma, jami’an rundunar ‘yan sanda sun tarwatsa matasan da su ka fita zanga-zangar juyin-juya-hali a yankin Ikeja ta hanyar harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa su, sai dai wasu daga cikin matasan sun tirje, inda su ka kwanta a kasa tare da rike takardun da su ke dauke da su.

A wani bangare kuma, rahotoanni sun ce jami’an ‘yan sanda sun kama matasa 60 daga cikin matasan da su ka fita zanga-zangar juyin-juya-hali a birnin Abuja.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *