Gwamnonin jihohin Nijeriya 36, sun yanke shawarar ganawa da
shugaba Buhari game da matsalar tsaro.

Bayan zaman kwamitin tsaro na kungiyar Gwamnonin, sun
yanke shawarar kai wa shugaba Buhari koken al’ummar su
dangane da halin rashin tsaro da ya ke kara tsananta.

Yayin bayyana damuwa game da harin da ake zargin ‘yan Boko
Haram sun kai wa ayarin motocin gwamna Zulum na jihar
Borno, sun nuna bacin rai a kan tabarbarewar tsaro duk da
kokarin gwamnatin tarayya.

Haka kuma, gwamnonin sun bayyana damuwa a kan yadda wasu
jami’ai biyu na rundunar hadin gwiwa da jami’in dan sanda daya
su ka raunata yayin maida martani a harin.

Gwamnonin sun cimma matsayar hakan ne, a cikin wata wasikar
jaje da su ka aike wa Zulum dauke da sa hannun shugaban
kungiyar Kayode Fayemi.

Fayemi ya ce, kwamitin tsaro na kungiyar gwamnonin ya shirya
gudanar da wani zaman musamman, inda daga nan za su zartar
da shirin ganawa da shugaba Buhari da hafsoshin tsaro.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *