Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya gargadi masu garkuwa da mutane da ɓarayin shanu da ‘yan bindiga su kiyayi jihar sa.

Yahaya Bello ya yi gargadin ne, yayin naɗin sarautar kwamishinan ma’adinai Injiniya Abubakar Bashir Gegu da wasu mutane 64 da Onyiwo na Gegu-Beki Mohammed Abbas ya yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce fushin iyaye da kakannin ‘yan kabilar Egbira zai faɗa a kan duk wanda ya nemi ya fara aikata laifuffukan da su ka hada da satar shanu da garkuwa da mutane da sauran su.

Gwamnan ya cigaba da cewa, ‘yan kabilar Egbira da su ka fito daga Kwararafa mutane ne masu yawa da ƙarfi kuma masu maraba da baƙi da kuma aiki tukuru da juriya.

Ya ce za su yi amfani da ƙarfin iyayen su da kankani wajen magance duk wata barazana, kuma su na da karfafan mazaje da mata da a shirye su ke su magance duk wata barazanar tsaro.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *