Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya kalubalanci masu rike da sarautun gargajiya a kudancin jihar da su nuna wani wuri da aka kwace a yankunan su aka mika ma wasu mutane ko kungiyoyi ba bisa ka’ida ba.

El-Rufa’i, ya kuma ya kalubalanci sarakunan da su ba hukumomi da jami’an tsaro goyon baya a kokarin su na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kudancin jihar Kaduna.

Haka kuma, ya zaburar da su a kan su zama masu adalci ga duk jama’ar da ke zaune a karkashin masarautun su.

El-Rufa’i ya bayyana haka ne a matsayin martani, dangane da zargin cewa wasu mutane sun kwace wasu sassan kudancin jihar Kaduna a ‘yan kwanakin baya-bayan nan.

Yayin ganawar sa da majalisar sarakunan jihar Kaduna, El-Rufa’I ya ce gwamnatin sa ta dauki duk mazaunin wani yanki a matsayin dan jiha kamar yadda kundin tsarin mulki ya amince.

Ya ce yada labarun karya a kan gaskiyar halin da kudancin Kaduna ke ciki ba zai kashe gwiwar gwamnatin sa a kokarin ta na kawo karshen rikicin da aka shafe kusan shekaru 40 ana fama da shi ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *