Wasu mata uku, ciki har da masu aikin jinya biyu sun shiga hannun jami’an ‘yan sanda na jihar Katsina bisa laifin sace wata jaririya.

Rahotanni sun ce, ana zargin matan da yunkurin sace wata jaririya da aka haifa,aka bar ta a wani asibitin kudi da ke Katsina.

Kamar yadda ‘yan sanda su ka bayyana, wata Shamsiya Sani da ke unguwar Dandagoro a Katsina ce ta haifi jaririya a ranar 25 ga watan Yuli na shekara ta 2020.

Sai dai matar ta gudu ne ta bar yarinyar da ta haifa kwance a gadon asibiti, dauke da takardar da ke nuna cewa ta samu cikin ta ne ba tare da mijin aure ba.

Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa, ma’aikatan jinya da su ka hada da wata Misira Tijani da Grace Ejigu sun dauke jaririyar sun saida ma wata Eucharia Onyema.

Yanzu haka dai an kama matan uku da ake zargi da satar jaririyar, an kuma gabatar da su a babban ofishin ‘yan sanda da ke Katsina.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *