Gwamnatin jihar Bauchi ta kafa dokar da ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa kananan yara Fyade.

Dokar, ta kuma tanadi ɗaurin rai da rai ga wanda ya yi wa babbar mace fyade da kuma ɗaurin shekaru 20 ga wadanda su ka yi wa mace daya taron dangi.

Wannan dai ya na zuwa ne, yayin da hukumomin ‘yan sanda a jihar su ka ce sun samu rahotannin aikata fyade 21 a cikin wata ɗayan da ya wuce kawai.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Bauchi DSP Muhammad Ahmad Wakili, ya ce tuni majalisar dokoki ta jihar ta amince da kuma za a wallafa ta.

A cewar sa, tsakanin watannin Yuli da Agusta sun gabatar da mutane 22 da ake zargi da aikata fyade a gaban ‘yan jarida.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *