Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta tura da karin jiragen ruwa na yaki 8 da na sama biyu domin yaki da ayyukan ta’addancin kan iyakokin ruwa.

Rundunar ta ce wannan mataki da ta dauka na daga cikin wani hobbasa da ta ke yi na yaki da ayyukan ta’addanci da suka hada da fashin teku da sauransu.

Kwamandan rundunar dake kula da shiyyar yamma, Rear Admiral Tanjuma Moses, bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na rundunar tsaro a Legas.

Ya ce tun bayan kaddamar da shirin kwanaki 11 da suka gabata rundunar sojin ta kwato jiragen ruwa biyu tare da kama wasu mutane takwas da ake kyautata zaton na da hannu a harkokin satar mai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *