Ministan lafiya Osagie Ehanire, ya ce ana ci gaba da fito da sabbin dabaru da za su taimaka wajen rage yawan mace-macen da cutar korona ke haddasawa da kasa da kashi 1 cikin dari.

Ehanire ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a wajen taron kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kan yaki da cutar kan yaki da cutar a Abuja.

A cewarsa a yanzu ana samun yawan mace-macen masu dauke da cutar da kashi biyu cikin dari, wanda kuma hakan yafi shafar wadanda suke da yawan shekaru da kuma masu wadansu cututtuka.

Ehanire ya ce kwamitin yaki da cutar ta korona ta cimma matsaya wajen tsananta aiki da matakan kariya da suka hada da tilasta amfani da takunkumin rufe baki da hanci da kuma gujewa taron jama’a.

Ministan ya kara da cewa akwai bukatar karawa tare da inganta dakunan gwaje-gwajen cutar dake fadin Najeriya, yayin da a yanzu ake gwada mutane dubu 40 a cikin wata guda.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *