Kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar koron da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na aikin fitar da ka’idojin da za a yi amfani dasu a zabubbukan dake tafe.

Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya bukaci shugabannin jam’iyyu, magoya baya da su kansu ‘yan siyasan su yi amfani da matakan kariya a kafin, lokacin da kuma bayan zabubbukan da za su gudana.

Mustapha ya kara da cewa kwamitin da yake jagora zai ci gaba da aikin kafada da kafada da jihohi domin wayar da kai kan matakan kariya daga kamuwa da cutar.

Ya kara da cewa kwamitin zai gabatar da rahoton wucin gadi na 6 kan yaki da cutar korona ga shugaban kasa Muhammadu Buhari nan bada jimawa ba.

Za a fara ne da zaben cike gurbi a jihar Nasarawa daga ranar 8 ga watan Augusta, inda daga baya za a gudanar da zabubbukan a jihohin Edo da Ondo a watannin Satumba da Oktoba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *