Gwamnatin tarayya ta ce an kashe sama da naira milliyan dari 5 da 23 a shirin ciyar da daliban makarantun gwamnati lokacin dokar takaita zirga-zirga domin yaki da cutar korona.

Ministar kula da harkokin jin kai da ci gaba ta Najeriya Sadiya Farouq ta bayyana haka a waken taron manema labarai da gwamitin yaki da cutar korona ke shiryawa a Abuja.

Ta ce an an kara fadada shirin tare da kaddamar da shi karin jihohi 3 na Najeriya tun bayan umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada ranar 29 ga watan Maris.

A cewar ta bincike da hukumar kididdiga ta Najeriya, da babban bankin Najeriya suka gudanar ya nuna an warewa ko wanne gida naira dubu 4 da dari 2.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *