Karamin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, ya umurci makarantu da su tattauna da iyayen yara kan rana da kuma lokacin da suke tunanin za su sake bude makarantunsu domin ci gaba da karatu.

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Ben Goong ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a karshen ganawar da ministan ya yi da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 dake fadin Najeriya.

Ya kara da cewa makarantun tarayya 104 sun shirya tsaf domin komawa karatu gadan-gadan daga yau 4 ga watan Augusta.

Ministan ya yaba da irin shirye-shiryen da makarantun gwamnatin suka yi gabannin komawa makarantun.

Ya ce kwamishinonin jihohin sun bayyana irin shirye-shiryen da suka yin a bude makarantu daga yau 4 ga watan Augusta zuwa 10 ga wata.

Ya kara da cewa ya zama wajibi a rika gwada zafin jikin duk wani Dalibi da zai shiga makarantun, domin tabbatar da lafiyarsa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *