Gwamnatin jihar Kano za ta yiwa makarantun gwamnati da masu zaman kansu dari 5 da 28 dake fadin jihar feshin magani gabannin zana jarabawar kammala makarantun sakandire na yammacin Afrika.

Kwamishinan ilimi na jihar Muhammad Sa’id, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bada umurnin yin feshin ne domin tabbatar da lafiyar dalibai da malamansu, da kuma samar da yanayi mai kyau na karatu.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta amince a sake bude makarantu ga dalibai dake ajin karshe daga ranar 10 ga wannan watan na Augusta da muke ciki.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kuma bukaci ma’aikatar kula da lafiya ta fara aikin raba takunkumin kariya daga cutar korona, sinadarin tsaftace hannu da aka fi sani da sanitizer, da kuma roba da ruwan wanke hannu a makarantun.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *