Gwamnatin Kaduna ta ce tana duba yiwuwar sake sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin jihar sakamakon yawaitar samun mutane dake dauke da cutar korona.

A lokacin da yake zantawa da wata kafar yada labarai, Gwamnan jihar Nasir Ahmad El-Rufai, ya ce rashin bin dokokin kariya da suka hada da sanya takunkumin kariya, da gujewa taron jama’a na daga cikin abubuwan dake haddasa yawaitar cutar a tsakanin al’umma.

Ya kuma nuna fargabar akwai yiwuwar cutar da yanzu hake ke karuwa ta fi ƙarfin asibitocin dake jihar ta Kaduna.

A baya dai, gwamnatin Kaduna ta sa dokar kulle fiye da tsawon wata uku kafin buɗe ta kuma yanzu haka jihar ita ce ta takwas a jerin jihohi masu fama da cutar korona.

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC dai ta ce a cikin kwanaki 3, cutar ta kama mutane 95 a jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *