Karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce makarantu masu zaman kansu na da ikon karbar kudin zangon karatu na karshe na daliban da suke shirin kammala karatu da gwamnatin ta amince musu su koma.
Nwajiuba ya bayyana hakan ne a wajen taron manema labarai da kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar korona ke shiryawa a Abuja.

Ministan na amsa tambayar da aka masa ne na cewa ko makarantun masu zaman kansu za su iya karbar kudin zangon karatu na karshe daga iyayen dalibai duk da cewa takaitaccen lokaci za su yi a makarantun.

Ya ce masu kamarantun suna gudanar da harkokin su ne a matsayin kasuwanci, ba wai tallafi ko wani abu makamancin hakan ba, a don haka suna da ikon yanke hukuncin da suke bukata akan hakan.

Nwajiuba, ya kara da cewa idan aka fara zana jarabawar kammala makarantar sakandire ta yammacin Afrika WAEC a ranar 17 ga wannan watan na Augusta, za a kammala zuwa watan Satumba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *