Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an sake gano masu cutar korona 288 a ranar Litinin din nan.

Cibiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter ta ce adadin wandanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan bullarta a watan Fabrairun wannan shekarar sun kai 44,129.

Ta ce masu cutar ta korona takwas ne suka rasa rayukansu a cikin sa’o’i 24, yayin da aka salami mutane 355 da suka warke daga cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi musu na baya-bayan nan ya nuna basa dauke da cutar.

Wannan dai shi ne adadi mafi ƙaranci cikin watanni biyu da hukumar NCDC ta fitar, a sabbin wadanda suka kamu da cutar tun bayan ɓullarta Najeriya.

An fara gano ƙwayar cutar korona a Najeriya ne a ranar 27 ga watan Fabrairu bayan wani dan kasar Italiya ya shigo ta filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *