Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun ya soke umurnin da gwamnatin jihar ta bada a baya na yiwa dukkanin dalibai da ke shirin komawa makaranta gwajin cutar korona.

Wannan na zuwa ne biyo bayan cece-kuce da aka samu daga iyayen yara na kudaden gwajin naira dubu 25 na kowanne yaro a makarantun kudi dake fadin jihar.

A wata sanarwa da ya fitar, gwamnan jihar ya soke kudirin da gwamnatinsa ta dauka a baya na yin gwajin cutar ga duk daliban da aka amince su koma makaranta.

Ya ce tsarin karbar daliban a dakunan kwana na makarantu masu zaman kansu ya rataya ne a wuyan iyaye da kuma hukumomin makarantun.

Gwamnatin jihar ta kuma bada shawarar cewa daliban da kwana a makarantun bai zama musu tilas ba, su rika zuwa daga gidajen su a kullum.A lokacin da yake bada hakuri kan maganar gwajin da ya yi a baya, gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta bada umurnin samar da takunkumin kariya daga cutar ta korona a dukkanin makarantun na gwamnati da masu zaman kansu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *