Gwamnatin jihar Katsina ta ce manyan jami’an ‘Yan sanda 30 ne kacal su ke ba daruruwan kauyuka tsaro a fadin jihar sa.

Gwamnan jihar Aminu Bello Masari, ya bayyana haka, a lokacin da ya gudanar da bikin babbar sallah tare da jami’an tsaron da ke filin daga a Katsina, inda ya ce jihar sa na fama da karancin jami’ai.

 Gwamnan, ya ce ya na kokarin ganin an yi wa dokokin kasa garambawul ta yadda kananan hukumomi za su iya magance matsalar da ake fama da ita.

Ya ce ‘yan bindiga sun saje da mutanen gari, don haka akwai wahala a iya bambamce tsakanin nagari da miyagu, kuma ko da jami’an tsaro sun fatattaki duk ‘yan bindigar wasu sababbin zubin miyagu za su bayyana a madadin su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *