Babban kantin saida kayayyaki na ‘Shoprite’, ya ce ya na duba yiwuwar barin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa, ta ce masu kantin sun dauki matakin janyewa daga Nijeriya ne saboda an samu mutanen da su ka nuna sha’awar sayen shi.

Shoprite ya bayyana Nijeriya a rukunin kasashen da zai daina gudanar da harkoki, yayin da ya sanar da raguwar sama da kashi 5 cikin dari na kasuwar sa a shekara ta 2019, da kuma kusan kashi 6 da rabi daga watan Janairu zuwa Yuni na shekara ta 2020 saboda annobar korona.

Babban kantin, ya ce annobar korona ta yi tasiri sosai a kan harkokin kasuwancin sa na kasashe 14 a Afirka, inda aka samu raguwar sayen kayan sa da kashi 1 da rabi, ko da ya ke a Afirka ta Kudu an samu gagarumar karuwar kasuwancin su.

Mai magana da yawun babban kantin a Nijeriya Mr. Ini Achibong, ya ce masu kantin sun dade su na neman mutanen da za su saye shi, kuma babu abin da zai sauya game da yadda ya ke gudanar da harkokin sa a wannan lokaci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *