Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa NEMA, ta kai dauki ga ‘yan gudun hijirar da tashe-tashen hankulan Boko Haram da fadace-fadacen kabilanci ya shafa a jihohin Adamawa da Taraba.

Ya zuwa yanzu dai, akwai ‘yan gudun hijira dubu uku da dari tara da talatin da shida a sansanonin Malkohi, da St. Theresa da kuma Fufore, wadanda rikicin Boko Haram ya raba da gidajen su a jihar Adamawa.

Jami’in hukumar Abubakar Sadik Nuhu, ya ce NEMA z a ta ci gaba da kai tallafin abinci ga ‘yan gudun hijirar a duk wata.

Daya daga cikin shugabanin ‘yan gudun hijira a sansanin Fufore Bakura Umar Mika, ya ce su na kira ga gwamnati ta taimaka masu da wurin zama da kuma jarin sana’o’i.

Bayan kai tallafin ga sansanonin ‘yan gudun hijira da tashin hankalin Boko Haram ya shafa, hukumar ta NEMA ta kuma kai tallafin musamman ga wasu da tashin hankalin kabilanci ya raba da gidajen su a yankin Guyuk da Lamurde da kuma jihar Taraba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *