Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya ce duk wanda ya ce zai yi amfani da karfi da yaji wajen yin magudin zabe zai ga tarzoma.

Da ya ke magana yayin da ya karbi bakuncin shugabannin addinin Musulunci a gidan gwamnati da ke Benin, gwamnan ya zargi Shugaban jam’iyyar APC na jihar da shigo da makamai domin tsorata magoya bayansa.

Ya ce a shirye ya ke ya tsaya da mutanen sa da kuma kare ra’ayoyin su, domin ba ya jin tsoron kowane mutum sai Allah,ya ce ya san ana yi ne don a tunzura shi da magoya bayan sa, amma ba za su fada tarkon makiya ba.

Obaseki, ya ce yanzu haka ‘yan sanda daga Abuja sun shiga jihar, wadan da wani attajiri ya dauki nauyin su don su kama magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar.

Ya ce su na shirin haddasa rikici ta hanyar shigar da makamai da domin tsoratar da magoya bayan su, saboda sun san idan aka yi zabe na gaskiya da amana ba za su kai labari ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *