Jami’an sojin Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga 80 tare da ceto mutane 17 da suka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso yamma.

Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata  sanarwar da ma’aikatar ta fitar,  inda ta ce dakarun sun samu nasarar ne bayan sun kaddamar da samame a kan ‘yan bindigar a jihohin Katsina da Zamfara da kuma Sokoto a ranar 31 zuwa 1 ga watan Agusta.

Ma’aikatar ta ce, a tsawon watan guda da dakarun su ka yi su na yaki da ‘yan bindigar, sun yi nasarar kwato shanu 943 da  tarin makamai da kuma kame mutane 14 da ke taimakawa ‘yan bindigar da bayanan asiri.

Kakakin ma’aikatar tsaron ya ce komawar manoma zuwa gonakin su a wasu sassan da a baya ke fuskantar barzanar ‘yan bindiga, ya tabbatar da cewa an samu nasara a yaki da ‘yan bindigar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *