Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya shiyyar jihar Kaduna, ta ce akan samu mutum guda a cikin 10 dake ta’ammuli da kwayoyi.

Shugaban hukumar Joseph Maigari ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a kan aikace-aikacen cibiyar, ya ce kididdigar da aka gudanar a wannan shekarar a kaduna ta nuna cewa, a cikin kananan hukumomin jihar 23, an samu mutane 11 cikin 100 da ke tu’ammuli da muggun kwayoyi.

Sai dai, ya ce hukumar na aiki da wasu kungiyoyi masu zaman kan su da ma’aikatun gwamnati wajen rage shan kwayoyi a fadin jihar.

Yaki da tu’ammuli da kwayoyi a Nijeriya ya kasance ana kama masu safarar kwayoyin, wanda hakan bai haifar da da mai ido, wanda hakan ya zama wajibi a janyo hankalin mutane su daina amfani da kwayoyi.

Jihar Kaduna dai, ta kasance jiha ta farko a Nijeriya da ke da doka mai tsanani a tu’ammuli da kwayoyi, kuma ta na gina gidajen gyara ‘yan kwaya a Ikara da Chikun da Igabi da kuma Kachia.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *