Gwamnatin Jihar Legas ta amince a sake bude wuraren ibada a daukacin jihar, bayan da su ka shafe watanni a rufe, domin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu, sanar da haka, ya ce matakin sake bude wuraren Ibadar zai soma aiki ne daga ranar 7 ga watan Agusta, amma da sharadin kashi 50 cikin 100 na adadin mutanen da filaye ko gine-ginen da wuraren ibadar za su iya dauka ke da izinin shiga cikin su.

Gwamnan, ya kuma sassauta dokar da ta haramta taron sama da mutane 20 zuwa sama da mutane 50, sannan ya shawarci dattawa masu shekaru 65 zuwa sama su kaurce ma wuraren ibada.

A watan Maris da ya gabata ne, hukumomin Legas su ka rufe coci-coci da masallatai da wuraren shakatawa da sauran su, a kokarin su na dakile yaduwar coronavirus.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *