Fadar shugaban kasa ta ce, kalaman da Mamman Daura ya yi game da wancakalar da tsarin karba-karba da ake yi a koma tsarin cancanta ra’ayin shi ne ba nata ba.

Wadannan kalamai dai sun tada kura a Nijeriya, ganin cewa Mamman Daura Dan-Uwa ne kuma makusancin Buhari na kut-da-kut.

Sai dai fadar shugaban kasa ta nesanta kan ta daga kalaman Mamman Daura, cewa ra’ayin sa ya fada a matsayin sa na dattijon Kasa amma ba ra’ayin shugaba Buhari ko jam’iyyar APC ba.

Mamman Daura dai ya ce Nijeriya ta yi kwarin da a yanzu za ta iya watsar da tsarin karba-karba a maida hankali wajen zaben wanda ya fi cancanta a shekara ta 2023.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *