Dan majalisar dattawa Ali Ndume, ya ce akwai bukatar mika shugabancin kasa ga dan kudancin Nijeriya a shekarar 2023.

Ndume ya bayyana matsayin sa ne, yayin wata zantawa da yay i da manema labarai, inda ya ce zai zama an yi adalci idan aka bari yankin kudu ya karbi shugabancin Nijeriya bayan cikar wa’adin shugaba Buhari a shekara ta 2023.

Ya ce ta bangaren jam’iyyar APC, ta na so Shugaban kasa ya fito daga yankin Kudu, kuma ya na sahun gaba a wannan yunkuri, domin duk inda babu adalci ba za a taba samun zaman lafiya ba.

Ndume ya cigaba da cewa, yayin kafa jam’iyyar APC, an mika shugabancin kasa ga yankin arewa, kuma zai zama adalci ne idan aka mika wa yankin kudu nan gaba.
Ya ce ba zai mara wa dan takara daga yankin arewa ba, kuma ba ya tunanin APC za ta goyi bayan dan takara daga yankin arewa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *