Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya janye wasu manyan jami’an ‘yan sanda da ke aiki a hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC.

Rahotanni sun ce kiranyen shugaban ‘yan sandan zai shafi akalla shugabannin shiyya 20 da ke hukumar EFCC.

An dai saki Ibrahim Magu ne bayan makonni biyu da fara binciken shi bisa zargin almundahana da kuma rashin biyayya kamar yadda ministan shari’a Abubakar Malami ya rubuta korafi a kan sa zuwa fadar shugaban kasa.

Tun bayan fara gurfanar sa a gaban kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa, Jami’an ‘yan sanda ne su ke kai shi fadar shugaban kasa duk lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin binciken domin cigaba da amsa tambayoyi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *