Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce wasu daga cikin jami’an da ya ba shugabancin hukumomin Nijeriya sun ci amanar da ya ba su.

Buhari ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai bayan gudanar da Sallar idi a Abuja, inda ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa shugabanni da manyan jami’an wasu daga cikin hukumomin gwamnatin sa da su ka hada da NDDC da EFCC.

Karo na farko kenan da shugaba Buhari ya yi tsokaci a kan binciken almundahanar kudade da kadarorin da aka bankado a hukumar raya yankin Neja Delta da ke karkashin Sanata Godswill Akpabio, da kuma hukumar EFCC da aka dakatar da mukaddashin shugaban ta Ibrahim Magu bisa zargin karkatar da kudaden da satar da aka kwato.

Har yanzu dai kwamitin binciken da gwamnatin tarayya ta kafa a karkashin mai shari’a Ayo Salami tsohon na ci-gaba da aikin gano gaskiyar tuhume-tuhumen da ake yi wa Magu.

A baya-bayan nan ne aka bankado bacewar kudaden da yawan su ya kai naira biliyan 40 a hukumar NDDC, lamarin da ya sa shugaba Buhari kafa kwamitin da zai binciki yadda aka tafiyar da hukumar tun daga shekara ta 2001 zuwa 2019.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Duk fa abun da shugaba Buhari ya yi ba zai fita ba kuma ba zai wanke kan shi ba. Wane irin shugaba ne zai bayar da aiki amma ya ja ya koma gefe ɗaya yayi gum ba zai bibiyi yadda ake gudanar da aikin ba don ya tabbatar an yi daidai ko ba yi ba? Idan makahon so zai hana hukunta shugaba Buhari a nan duniya, a lahira Allah Azza wa Jalla ba zai bar shi ba. Buhari ya ba mu mamaki. Wata sakayya sai Allah.