Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, ya ce Nijeriya ta na karbar bashi daga kasar China ne saboda ya fi sauki ta fanin kuɗin ruwa da wa’adin biya da hukuncin saɓa lokacin biya idan an kwatanta da sauran ƙasashen Yamma.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na AIT, Ministan ya ce idan Nijeriya ta daina karbar bashi hakan ya na nufin ayyukan gine-gine da gwamnatin tarayya ke yi za su tsaya cak.

Ya ce, mutane su na tambaya ko Nijeriya za ta iya biyan basukan da ta ke ci, ya na mai bada tabbacin cewa za ta biyadomin ‘yan kwangila ake biya kuɗin kai tsaye da zarar an sa hannu cewa sun yi aikin.

Ameachi ya kara da cewa, in da gwamnatocin baya sun yi ayyukan gine-gine da batun ciwo bashin ma bai taso ba a yanzu, don haka ya kamata Majalisar Tarayya da ‘yan Nijeriya su yarda cewa ana samun ci-gaba ta fannin gine-gine.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *