Mutane goma sun mutu aka kuma ceto biyar, yayin da wasu hudu su ka bace sakamakon kifewar wani kwale-kwalen daukar fasinja a Lagos kamar yadda hukumomi su ka bayyana.

A cikin wata Sanarwa da hukumar kula hanyoyin ruwan jihar Lagos ta fitar, ta ce kwale-kwalen ya na kan hanyar sa ta zuwa Badagry ne daga gidan yarin Kirikiri, inda kwatsam igiyar ruwa ta yi ma shi dabibaiyi.

Sanarwar ta ce, jimillar mutane 19 ne a cikin cikin kwale-kwalen, aka kuma yi rashin sa’a akasarin fasinjojin da ke ciki ba su sanye da rigar kariya.

Hukumar kula da hanyoyin ruwan ta kama matukin jirgin ruwan ta kuma mika shi ga ‘yan sandan da ke kula da sufurin ruwa domin ci-gaba da bincike.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *