Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya cika duk alkawuran da ya yi wa ‘yan Nijeriya a shekara ta 2015.

Bagudu ya bayyana haka ne a jawabin sa na barka da sallah, inda ya ce an samu saukin matsalolin tsaro fiye da lokacin da Buhari ya hau karagar mulki.

Ya ce Nijeriya ta samu gagarumar nasara a yaki da cin hanci da rashawa, ya na mai yaba wa shugaba Buhari bisa amincewar da ya yi wa ministan shari’a Abubakar Malami.

Bagudu ya kara eda cewa, jami’an tsaro su na iyakar kokarin su wajen tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya, wanda yanzu haka babu  wani yanki da ke karkashin ikon ‘yan ta’adda.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *