Hukumomi a jihar Neja sun kaddamar da bincike don gano dalilin mutuwar wasu ‘yan mata bakwai da sanyin safiyar ranar juma’a 31 ga watan Yuli, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da idin Babbar Sallah.

Lamarin dai ya faru ne a garin Rijau, inda rahotanni su ka ‘yan matan shida sun je wani shago ne da ake gyaran gashi domin yin kitson sallah, amma daga bisani sai dai aka ga gawarwakin su tare da mai gyaran gashin.

Shugaban karamar hukumar Rijau Bello Bako, ya ce ya bada umurnin a yi wa yaran jana’iza kafin daga bisani a cigaba da bincike, yayin da daya daga cikin iyayen yaran Alhaji Abdulrazak Rijau, ya ce iyakar abin da ya sani shi ne yaran sun tafi kitso, kawai sai dai aka kira shi aka shaida ma shi abin da ya faru.

Rudunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakin ‘yan sanda na jihar ASP Wasiu Abiodun ya ce su na kan bincike.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *