Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana tababa a kan harin da aka kai ma tawagar motocin sa a garin Baga yayin wata ziyara da ya kai.

Ya ce lamarin ba na rashin isassun ma’aikata ko rashin kayan aiki ba ne, zagon ƙasa ne kawai tsagoran sa, don haka kada mutane su ƙalubalanci Shugaba Buhari ko Janar Buratai.

Zulum ya kara da cewa, duk da haka ya kamata a sake duba yadda ake bada umarni dangane da wannan aiki, kuma irin wannan harin ba zai sa shi ya karaya ba.

Bayan harin na Baga, an kuma kai wani hari a kan wata tawagar da ke share wa gwamnan hanya da ake kira Advance Party.

Mataimakin Kakakin Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Borno ASP Yakubu Mohammed, ya ce su na sane da harin, sai dai ba su da cikakken rahoto a kai, amma a cikin rahotannin da su ka samu babu kisa, kuma har yanzu su na tattara bayanai a kan lamarin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *