Rundunar Sojin Nijeriya ta sallami sama da jami’ai 300 a kan laifin gudu daga faggen yaki da ‘yan Boko Haram na rundunar Operation Lafiya Dole.

Binciken ya nuna cewa, kwamandojin rundunar ne su ka sallami Sojin tsakanin shekara ta 2015 da 2016.

Haka kuma, binciken ya ce bayan masu laifin gudu daga fagen daga, an sallami wasu a kan laifin amfani da takardun karatu na bogi, da lambar BVN ta bogi da wasu laifuffuka.

Bayanan sun nuna cewa, an sallami Sojojin Bataliya ta 118 a ranar 13 ga watan Disamba na shekara ta 2015, bisa laifin kin shiga motar yaki daga Maimalari zuwa Baga.

Sojojin dai sun yi korafi a kan motar, kuma saboda haka sun kwashe kwanaki biyar su na tattaki zuwa fagen fama a Baga domin kwato ta daga hannun Boko Haram, bayan sun isa Baga ne kwamandan su Kanar S. Omolori ya tuhume su da laifin tserewa, inda ya sallami 24 daga cikin su.

Bincike ya nuna cewa wasu Sojojin da aka sallama sun kalubalanci hakan inda su ka zargi kwamandojin su da zalunci, sannan sun bukaci babban hafsan Sojin Nijeriya Janar Tukur Buratai ya maida sub akin aiki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *