Rundunar Sojin Nijeriya za ta fara bincike a kan harin da aka kai wa tawagar Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno.

Mai Magana da yawun rundunar sojin Sagir Musa ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su ka kai wa tawagar gwamnan hari a hanyar su ta zuwa garin Baga.

Ya ce Zulum ya ziyarci Kwamandan Brigade ta 19 na Rundunar Soji da ke Sansanin Baga, inda ya yi ma shi bayani a kan halin tsaro na yankin baki daya.

A cewar sa, mummunan lamarin ya faru ne jim kadan bayan gwamnan da tawagar sa sun bar sansanin sojojin za su ziyarci wasu yankuna a garin ta Baga, lamarin da ya tilasta wa gwamnan soke ziyarar da ya yi niyyar kaiwa a wasu sassan yankin.

Ya ce duk da cewa a halin yanzu babu cikaken bayani a kan harin, amma ana kokarin bincike a yankin da abin ya faru da niyyar gano wadanda su ka kai harin, ya na mai bayyana harin a matsayin abin takaici.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *