Kwamandan Sojojin ‘Operation Safe Haven, Chukwuemeka Okonkwo, ya ce kashe-kashen da ke faruwa a Kudancin Kaduna wasu mabarnatan Fulani da kabilun yankin ne ke yi a tsakanin su, amma ba kisan-kare-dangi ba ne kamar yadda wasu ke ikirari.

Manjo Janar Okonkwo ya bayyana wa manema labarai haka ne bayan fitowar su wani taron musamman a kan matsalar tsaro a Kudancin Kaduna, inda ya ce abin da ke faruwa shi ne, idan an kai hari a wannan yanki, su ma sai su kai hari a wancan yankin.

Ya ce maganar gaskiya kowane bangare ya na kai hari a kan wani bangare, amma ba a jin rahoton barnar da ake yi wa wani bangare, watakila kuma yawancin gidajen jaridu ba su san cewa ana kashe kowane bangaren kabilun da ke rikicin ba.

Janar Okonkwo, ya ce akwai tantiran matasan Katafawa ‘yan-sara-suka, sannan akwai Fulani mahara da wasu tsagerun gari a kowane bangare, yayin da wasu mutane ke amfani da matsalar tsaro su na kai wa jama’a hare-hare.

Ya ce ana zaman gaba da kullatar juna tsakanin kabilun yankin da Fulani, domin abu kadan zai tashi sai su fara kai wa juna farmaki, baya da matsalar satar shanun Fulani.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *