Masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a Nijeriya, sun bukaci a dage ranar zana jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta WAEC, domin a cewar su hakan zai bada damar a kauce wa faduwar dalibai jarrabawar.

Hakan dai ya na zuwa ne, bayan da hukumomi sun fitar da sanarwa a kan ranar sake bude makarantu ga daliban da za su zana jarrabawar WAEC.

Hukumar tsara jarrabawar, ta ce ranar 17 ga watan Agusta ne za a rubuta WAEC, inda aka ba yaran akalla wa’adin makonni biyu su kimtsa.

Iyaye da dalibai da masana harkokin ilimi da malamai ne su ka bukaci a dage ranar rubuta jarrabawar, su na masu cewa makonni biyu sun yi wa yaran kadan su shirya yadda ya kamata.

Daraktar cibiyoyin zamantakewa a ma’aikatar kula da ayyukan addinai kuma tsohuwar malamar makaranta Bilkisu Muhammad Kaikai ta bayyana wa manema labarai cewa, a ganin ta yin hakan zai zama takura ga dalibai.

Ta ce idan yara su na gida, yawancin su ba karatu su ke yi ba, don haka ya kamata a dan bude makaranta na wani dan lokaci domin su tuna abubuwan da aka koya masu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *