Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Muhammadu Buhari zai gudanar da Sallar Idin Babbar Sallah ta bana a gida dashi da iyalansa kamar yadda ya yi a karamar Sallah.

Mai ba shugaban kasan shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanar da ya fitar a Abuja.

Mai ba shugaban shawara ya ce matakin da shugaban kasan ya dauka na zuwa ne a matsayin biyayya ga shawarar da majalisar koli kan harkokin addinin Musulunci ta bada.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na taya al’ummomin Musulmi murnar zagayowar babbar Sallah, tare da yin kira gare su da su gudanar da Sallar cikin bin ka’idojin kariya daga cutar korona.

Sanarwar ta ce shugaban ba zai karbi gaisuwar Sallah daga shugabannin addini na siyasa da sauran al’ummomi ba kamar yadda aka saba kaiwa a baya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *