Gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da kasar Isra’ila na samarwa tare da inganta harkokin wutar lantarki a Najeriya ta hanyar amfani da tsirrai.
An cimma matsayar kulla yarjejeniyar ce bayan ganawar sirri da aka yi a tsakanin Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya Ogbonnaya Onu, da mataimakin jakadan kasar ta Isra’ila a Najeriya Yotam Kreiman.
Jakadan ya nuna jin dadinsa bisa yarjejeniyar da aka cimma wanda a cewarsa kamfanin samar da wutar lantarki wanda aka shiga ganawar dashi na daya daga cikin kamfanonin dake gaba-gaba wajen samar da wutar lantarki a kasarsa.
A cewarsa kamfanin ya shahara wajen samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da tsirrai a fadin kasar.
A nasa jawabin ministan kimiyya da fasaha na Najeriya Onu, ya yabawa kasar Isra’ila, bisa irin ci gaban da ta samu a bangaren kimiyya da kuma fasaha.
Ya ce kasar Isra’ila ta kan cimma duk wani abu da ta sanya a gaba cikin sauki musamman a bangaren kimiyya da fasaha, sannan ya nuna jin dadinsa da yarjejeniyar da aka cimma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *