Ministan kula da harkokin sufurin jiragen kasa Rotimi Amaechi, ya umurci jami’an tsaro dake aiki a tashoshin jiragen na Abuja zuwa Kaduna da kada su bar duk wanda bai sanya takunkumin kariya daga cututtuka ba ya shiga harabar.
Amaechi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido kan irin matakan kariya daga cutar korona da fasinjojin jirgin ke dauka a lokacin tafiye-tafiyen.
Ziyarar ta ministan na zuwa ne bayan sake bude sufurin jiragen kasa da suka kwashe sama da watanni 4 a rufe domin dakile yaduwar cutar ta korona.
Da yake magana akan kudin jirgin, ministan ya ce gwamnatin tarayya ba ta da isashen kudaden da za ta yi amfani dasu wajen daidaita farashin kamar yadda ta saba yi a baya.
Ya ce fasinjojin jirgin basu bukatar wani horo na musamman domin ba kawunansu kariya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *